Connect with us

Labarai

Ba za mu yi watsi da tubabbun yan Daba ba- Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusif ta bayyana cewa ba za ta yi watsi da matasan da suka tuba daga harkar fadace fadacen daba ba, domin kuwa suna da baiwar da suke da ita wacce za ta amfanar da al’umma muddin aka basu kulawar da ta dace.

Kwamishinan Yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron da aka shirya domin karɓar wasu daga cikin matasan da suka yanke shawarar barin harkar daba.

In da ya ce zuwa yanzu an tantance matasa sama da dubu 1 da 600 da aka saka cikin shirin Safe Corridor, kuma nan gaba kadan za’a ci gaba da tantance wasu matasa 2,100 domin su ma su shiga cikin shirin.

Da yake nasa jawabin a madadin maimartaba sarkin Kano Dan Amar din Kano Alhaji Aliyu Harazimi ya bukaci Matasan da su dage wajen komawa ga Allah, domin hakan yana kawar da mutane daga aikata abubun da basu dace ba.

Taron  wanda ya kasance karo na uku da kwamishin na yada labarai da harkokin cikin gida na kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya jagoranta a  zaman tattaunawa da kwamitin zaman lafiya na safe Corridor domin cigaba da tattance su da kuma samar da hanyoyin cika musu alkawarin da gwamnatin kano ta dauka a kansu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!