Connect with us

Labarai

Ba zan yi babban shagali a bikin ranar haihuwa ta ba – Tinubu

Published

on

Shugaba Tinubu

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa zai gudanar da bikin cika shekaru 74 cikin sauƙi, la’akari da halin da ƙasa ke ciki da kuma ƙalubalen da ake fuskanta.

 

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, ya gode wa ‘yan Nijeriya bisa addu’o’i da fatan alheri, yana mai cewa goyon bayansu na ƙara masa ƙarfi wajen jagorantar ƙasar.

 

Tinubu ya amince cewa sauye-sauyen da gwamnatinsa ta aiwatar sun haifar da ƙalubale, amma ya ce ana fara ganin haske a ƙarshen rami duk da matsin lamba daga rikice-rikicen duniya.

 

Ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su ci gaba da haɗin kai da goyon baya, yana mai alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta cigaba da aiki tukuru domin gina ƙasa mai ɗorewa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!