Connect with us

Labarai

Babban joji na kasa ya rantsar da sabbin alkalai

Published

on

Babban jojin kasar nan Tanko Muhammad zai rantsar da sabbin alkalai guda tamanin da biyar a gobe Alhamis wadanda za su gudanar da shari’a a kotunan karbar korafe korafen zaben cike gurbi na jihohin Edo da Ondo da sauran zabukan da za a gudanar a sassan kasar nan.

Mai magana da yawun kotun daukaka kara, Hajiya Sa’adatu Kachalla ce ta bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Laraba.

Sanarwar ta bayana cewa, za a gudanar da rantsuwar a babban dakin taro na kotun kolin kasar nan da ke birnin tarayya Abuja a gobe Alhamis.

Za dai a gudanar da zaben cike gurbi a jihar Edo a ranar sha tara ga watan Satumbar da muke ciki, yayin da na jihar Ondo za a gudanar da shi a ranar goma ga watan Oktoba mai kamawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv

Now Streaming

Archives