Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Siyasa

Babbar kotun jahar Rivers ta umarci Lai Muhammad kada ya sake buga sunan Uche Secondus cikin wadanda suka barnata dukiyar kasa

Published

on

Babbar kotun jahar Rivers dake birnin Port Harcourt ta bayar da umarni ga Ministan yada labarai Lai Muhammad da kada ya sake buga sunan shugaban jamiyyar PDP Uche Secondus a cikin wadanda suka barnata dukiyar kasar nan.

Amma wadanda akai kara ko wakilansu basu halacci zaman kotun ba, amma a nasa bangaren babban mai sharia na jahar Rivers Justice Iyayi Laminikara ya umarci wadanda sukai kara da su sanar da wadanda akai kara ta hanyar da ta dace.

A ranar 31 ga watan Maris ne shugaban jam’iyyar PDP Uche Secondus yayi karar ministan yada labarai Lai Muhammad da ya nemi afuwar buga sunansa da yayi a cikin wadanda sukayi almundahana da dukiyar kasa ,sannan ya biya shi dala biliyan daya da miliyan dari biyar a matsayin bata masa suna.

Kotun ta daga shariar zuwa 28 ga watan Mayu .

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!