Siyasa
Jam’iyyar APC ta karawa zababbun shugabannin shugabanninta wa’adin shekara 1
Jam’iyyar APC mai Mulkin Najeriya ta karawa zababbun shugabannin ta da suka hadar da shugaban jam’iyyar na kasa Chief John Odigie-Oyegun wa’adin tsawon shekara guda.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da kwamitin zartaswar jam’iyyar ya fitar a Abuja.
Sanarwar tace karin wa’adin zai fara aiki ne daga ranar talatin ga watan Yunin shekarar 2018.
A baya-bayan nan ne shugaban jam’iyyar na kasa Chief John Odigie-Oyegun suka yi wata ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari, biyo bayan rahoton da jagoran jam’iyyar na kasa Bola Tinubu ya mikawa shugaba Buhari.
Rahotanni sun bayyana cewa cikin rahoton ana zargin Chief John Odigie-Oyegun da yiwa yunkurin sasanta rikicin cikin gida da ya kunno kai a tsakanin mambobin jam’iyyar kafar angulu.