Labarai
Babu gudu ba ja da baya kan sabuwar dokar haraji – Tinubu

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya yi watsi da kiran da wasu kugiyoyi ke yi na dakatar da aiwatar da sabbin dokokin haraji da ya jaddada cewa dokokin za su fara aiki ranar daya ga Watan Janairun Sabuwar shekarar 2026.
Sabbin dokokin harajin sun haifar da muhawara mai zafi a fadin kasar bayan zargin da ake yi cewa kwafen dokokin da aka fitar a hukumance sun bambanta da wadan da majalisar tarayya ta amince da su.
Kungiyoyi da dama ciki har da kungiyar lauyoyi kasar nan ta NBA da kungiyar kwadago ta kasa NLC sai kungiyar akantoci ta kasa ANAN da ta Dalibai NANS sun nemi a dakatar da aiwatar da dokokin har sai an warware matsalolin da ake zargi.
Sai dai Shugaba Tinubu ya ce babu wani abu da zai hana ci gaba da gyaran tsarin harajin a ranar daya ga watan Junairun 2026.
You must be logged in to post a comment Login