ilimi
Babu malamin da yake bin mu bashin albashi a Kano – Ƙiru
Gwamnatin jihar Kano ta ce, babu wani malami da yake bin ta bashin ko kwabo na albashi.
Kwamishinan ilimi Malam Sanusi Sa’idu Ƙiru ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Freedom Radio.
“Duk Najeriya babu inda malami ke jin daɗi sama da jihar Kano, domin kuwa muna biyan albashi a kan lokaci kuma bama hana albashi idan aka kwatanta da wasu jihohin ƙasar nan”.
Ƙiru ya kuma ce, suna sane da koken ƙungiyar malamai ta NUT na cewa wasu daga cikin malaman su sama da dubu 14 ba su da shaidar koyarwa ta TRCN.
“Mun nemi gwamna Ganduje ya sahale mana mu basu horo, kuma ya amince ya bamu naira miliyan 10 muka tsara musu wani horo kuma jarrabawa ta fito kuma sama da malamai dubu 12 sun samu nasara.
Ƙiru ya kuma ce, gobe Talata ce ranar malamai ta duniya kuma sun shirya taro da za su karrama wasu malamai don ƙarfafa musu gwiwa kan harkokin ilimi.
You must be logged in to post a comment Login