Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje ya fara daukar Malaman da zasu yi koyarwa a makarantun Tsangayu

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta fara daukar Malaman makarantun tsangayu aiki.

Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Muhammad Sanusi Kiru ne ya bayyana haka yayin taron kaddamar da fara daukar Malamai wadanda zasu yi koyarwa a makarantun tsangayu wadanda gwamnatin Kano ta kafa.

Ya ce gwamnati ta karbe iko da wasu makarantu guda uku wadanda tun farko gwamnatin tarayya ta gina a nan jihar Kano.

“Zamu dauki sabbin Malamai guda sittin wadanda zasu hadu da sauran malaman da muke dasu domin koyarwa a makarantun tsangayu da ke jihar Kano.”

“A yanzu haka muna da makarantun tsangayu guda goma Sha biyar kenan idan aka hada da guda goma Sha biyu da muke dasu a baya, Wanda kuma suna da dalibai sama da dubu biyu”

Kwamishinan ilimi na jihar Kano ya kuma ce tsarin daukar Malaman baya bukatar wani talarda.

Abinda kawai ake bukata shine mutum ya kasance hafizi ne.

Da ya ke gabatar da jawabi shugaban hulumar kula da makarantun Tsangayu da Islamiyu ta jihar Kano, Gwani Yahuza Gwani Dan Zarga, ya ce, a yau ka fara tantance malaman wadanda za a turasu makarantun da ke Bunkure da Bagwai da Kanwa.

Ya kuma ce gwamnati ba ta haramta makarantun allo a jihar Kano ba amma za a sabunta su ne domin su dace da zamani.

A cewar gwani Yahuza gwani Dan Zarga makarantun a matakin firamare suke kuma duk dalibin da ya kammalasu zai halarci makarantun sakandire domin ci gaba da karatunsa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!