Nishadi
Babu manhajar da ta kai Tik-tock samar da aikin yi -SMAPDA

Kungiyar wayar da kan matasa kan yadda za su ci gajiyar arzikin da ake samu a kafafen sadarwar zamani musamman kafar TikTok wato Social Media Awareness and Promotion Development Association (SMAPDA) ta ce idan har mutanan Arewacin Najeriya su ka yi amfani da fasahar da suke da ita wajen neman kudi a kafar ta TikTok da matasa da dama sun samu ayyukan yi da zai sa su rinka yiwa kamfanoni Tallace-Tallacen da za su samu kudi masu yawa.
Sakataren Kungiyar Kwamred Shamsuddin Bature, ne ya bayyana hakan yayin taron kwanaki biyu don wayar da kan masu amfani da manhajar musamman matasa ta yadda za su yi amfani da manhajar wajen neman kudi.
An fara gudanar da taron ne a ranar 21 inda za a kammala a ranar 22 ga watan Fabrairun shekarar 2025.
Masu amfani da manhajar da dama ne dai suka halarci taron da suka hadar da Nazakiya da Badoo da Bilkisu Billy da Warkal da Yaron Malam da Bala Billy’O da dai sauran su.
A zantawar Freedom Radio da wasu daga cikin mahalarta taron sun bayyana yadda za su yi amfani da baiwar da suke da ita a kafar wajen neman kudi.
Masu amfani da kafar a jihohin Arewacin kasar nan harma dana kudu da dama ne dai suka halarci taron da za a kwashe kwanaki biyu anayi.
You must be logged in to post a comment Login