Connect with us

Labarai

Matasa su rungumi Kasuwancin Internet -Dakta Kabiru Sufi

Published

on

Malami a kwalejen ilimi da share fagen shiga jami’a ta Kano CAS Dokta Kabiru Sufi, ya ce matasa na da damar samarwa kansu ayyuka da sana’o’i, matukar suka yi amfani da kafafen sadarwa na intanet wajen gudanar da kasuwancin zamani.

Dokta Kabiru Sufi, ya bayyana haka ne yau yayin wani taron karawa juna sani da cibiyar PR Nigeria tare da hadin gwiwar gidauniyar tunawa da Habiba Jimeta suka shiryawa ‘yan jarida, kan yadda za a yi amfani da kafafen sadarwa na zamani a wannan hali da ake ciki na fama da cutar Corona.

Labarai masu alaka.

Ana tafka kurakurai wajen amfani da Internet- kungiyar Smart Clicks

Matar da ta makance sakamakon kashe ‘’yayanta sojoji biyu ta samu taimako ta kafar sada zumunta

Dakta Kabiru Sufi, ya ce duk da kalubale da ake fuskanta a sadarwa ta Zamani , kafafen sadarwar wata dama ce ta samar da hanyoyin bunkasa kasuwanci ba tare da haduwa da juna ba, ta hanyar zaurukan tallata kaya.

A na sa jawabin ya yin taron  shugaban cibiyar PR Nigeria Adnan Mukhtar Tudunwada, ya ce sun shirya taron ne musamman ga ‘yan jarida kasancewar su jakadun al’umma, tare da wayar da kan matasa wajen amfana da kafafen sadarwar.

Masana da dama ne suka gabatar da makala kan yadda za a yi amfani da kafafen sadarwar na zamani wajen kasuwanci da yadda za a kaucewa kalubale, g dimbin matasan da suka halarci taron na yau.

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 331,665 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!