Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Babu wanda ya mutu a rikicin Bauchi

Published

on

Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta musanta rahoton da dan majalisar dokokin jihar Gazali Wunti ya gabatar da ke cewa an samu asarar rayuka a wani rikici da akayi a iyakokin karamar hukumar Ganjuwa da karamar hukumar Dikku ta jihar Gombe.

Mai magana da yawun rundunar Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da manema labarai.

Yace wasu mutanen karamar hukumar Dukku ne suka shiga gonakin manoman karamar hukumar Ganjuwa, wanda hakan ya jawo hatsaniya .

Tun da fari dai dan majalisar mai wakiltar Ganjuwa ta gabas ya gabatar da rahoton cewa al’ummar yankin Dukku sun kai hari wani kauye a mazabar Gungura wanda yai sanadiyar rasa rayuka.

A cewar wakil babu rahoton asarar rai a arangamar da suka yi kamar yadda aka fitar da rahoto a baya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!