Labarai
Bai kamata shugaba Tinubu ya saurari Kwakwaso ba- Jam’iyyar NNPP

Jam’iyyar NNPP ta ce, bai kamata shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mayar da hankali wajen sauraren dan takarar Jam’iyyar a zaben da ya gabata na shekarar 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba.
Ta cikin wata sanarwa da Sakataren Jam’iyyar na kasa, Olaposi Oginni ya fitar a ranar Lahadi, ya ce, kwankwaso ya fadi haka ne domin tayar da kura a fadin Najeiya.
Haka kuma, jam’iyyar ta bayyana kalaman Sanata Kwankwaso na cewar shugaban kasa Bola Tinubu ya yi watsi da yankin Arewa wajen samar da ayyukan more rayuwa ba gaskiya ba ne, zance ne da ba shi da tushe bare makama.
Olaposi ya kuma bayyana tsohon gwamnan na Kano a matsayin wanda ya rude a siyasa, saboda haka ne ma ya ke kokarin bata ayyukan alheri da shugaban kasa ke gudanarwa a yankin Arewa.


You must be logged in to post a comment Login