Connect with us

Labarai

Bamu rufe titin unguwar Dorayi ba – ‘Yansandan Kano

Published

on

Bamu rufe titin unguwar Dorayi ba – ‘Yansandan Kano

Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta karyarta wani labari da ake ta yadawa a kafafan sada zumunta na zamani wanda ke cewar rundunar ta rufe hanyar zuwa unguwar dorayi a safiyar yau Lahadi.

Cikin wata tattaunawa da kakakin rundunar DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa yayi da Freedom Radio ya bayyana mana cewa wasu al’ummar yankin ne suka nemi iznin hukumar domin gudanar da wasan tseren keke, inda hukumar ta sahale musu yin wasan, har ma ta hada musu da tawagar jami’an tsaro domin su sanya idanu kan yadda wasan zai kasance.

A don haka jami’an tsaron da aka gani a titin sunje ne kawai don sanya idanu ba don su rufe hanya ba.

 

Allah ya kyauta.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!