Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Bankin CBN ya ce sama da manoma 250,000 ne suka ci gajiyar bashin biliyan 55  a shekaru biyu

Published

on

Babban Bankin Najeriya CBN ya ce sama da manoma dubu dari biyu da hamsin ne suka karbi naira biliyan 55  a tsakanin shekaru biyu domin aiwatar da shirin bayar da rance ga manoma wato Anchor borrower.

Mukaddashin Daraktan yada labaran babban Bankin Isaac Okorafor ne ya bayyanan hakan yayin taron manema labarai kan fara aiwatar da shirin da ya gudana a larabar da ta gabata a birnin tarayya Abuja.

Ya kuma ce an fara kaddamar da shirin bada rancen ne a jihar Kebbi tun a ranar shabakwai ga Nuwambar shekarar 2015, wanda shugaban kasa Muhamadu Buhari ya kaddamar.

Haka kuma an kirkiri shirin ne domin a kulla alakar kasuwanci tsakanin manoma da kuma masu samar da kayan, inda ya ce bawai kawai a kara habaka harkar noman shinkafa da alkama ba, har ma da kara kulla alaka tsakanin manona da masu saya.

Okorafor ya ce cikin naira milyan 55 da babban bankin ya samar ga manoman kashi tamanin na kudun wato naira biliyan 44 an bada su ga manoman shinkafa ne

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!