Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugaban Buhari ya yi ganawa ta musamman da jagororin Jihar Katsina

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wata ganawa ta musamman da jagororin Dattijan Jihar Katsina a gidansa na Daura dake jihar ta Katsina.

Shugaba Buhari ya yi wannan tattauawa ne a jiya Lahadi, inada ya gana da Gwamnan Jihar ta Katsina Aminu Bello Masari da Sarkin Daura Alhai Umar Faruk da Galadiman Katsina kuma tsohon shugaban kotun daukaka kara ta tarayya Justice Mamman Nasir.

Haka zalika shugaba Buhari ya gana da Sarkin Maradun a Jihar Zamfara Alhaji Muhammad Tambari, wanda ya ziyarci shugaban kasar a garin Daura domin mika sakon ta’aziyyarsa bisa rasuwar wasu ‘yan-uwan shugaban kasar guda biyu.

Shugaban kasar wanda ya ke ziyarar kwanaki biyar a garinsa na Daura, ya gudanar da wata ganawar sirri da ‘yan-uwansa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!