Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Bankin CBN ya fara biyan tallafin Covid-19

Published

on

Central Bank Of Nigeria

Babban bankin kasa (CBN),  ya ce, wadanda suka samu nasarar cin gajiyar  bashin tallafin corona na naira biliyan hamsin da bankin ya ware, za su fara karbar sakonnin waya na biyansu kudaden, cikin awanni arba’in da takwas.

A cewar bankin na CBN duk wanda ya mika da bayanan asusun aji yarsa na banki, zai samu sakon shigowar kudin, idan kuma bai samu sakon turo mishi da kudin ba, zai iya tuntunar masu kula da shirin.

Haka zalika bankin na CBN ya kara da cewa, shirin na nan yana ci gaba da wakana, saboda haka duk masu sha’awa za su iya yin rajistar cin gajiyar tallafin kai tsaye ba tare da neman wanda zai tsaya musu ba.

CBN zai fara aiwatar da shirin Cash less

CBN ya gargadi bankuna kan kyautatawa abokan hurda

Bankin na CBN ya kuma ce, a Kason farko na wadanda suka samu nasarar cin gajiyar kudin, wanda adadinsu ya kai, mutane dubu goma sha hudu da dari uku da talatin da daya.

Ya kuma ce za a biyasu naira biliyan goma da miliyan dari tara, yayinda tuni kuma an biya mutane dubu biyar da dari takwas da sittin da takwas daga cikinsu, naira biliyan hudu da miliyan dari daya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!