Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Bashi ya sanya wata mace kamuwa da ciwon zuciya a gidan Kurkuku

Published

on

Masana da dama a fannin shari’a sun hakikance da cewar hakkin bayar da belin wanda ake tuhuma alhaki ne na alkali, to amma ido ba mudu ba ai ya san kima, domin a lokuta da dama za ka ga an kai mutum gaban alkali ana zarginsa da aikata wani babban laifi amma sai ka ga an bayar da belinsa musamman ma idan akwai Magan.

Haka kuma sai ka ga mutum ya yi laifin dan kankani amma sai ka ga ana artabu da alkali kan bayar dashi beli, a irin wananan ne discretion wasu alkalan ke aiki.

Wannan wata Magana ce mai jela za mu cigaban da janjanin ta a shirye shiryen mu na gaba.

A zancen nan da nake mu ku dai wata mata mai suna Maryam ce ta ci bashin abokan huldar ta, har ta kai sun mika ta ga ‘yansanda wane tudu wane gangare sai gashi an gurfanar da ita a kotun majistri mai lamba 72 karkashin mai sharia Aminu Gabari.

Fadin sunan Aminu gabari dai na san me sauraro zai iya tuna shi domin shi ne dai alkalin da aka kaiwa dalibin jamiar nan ta Bayero wanda wani dan majalisa ya yi zargin yake ta masa irli, kuma duk wani godo na neman belin dalibin Aminu gabarin bai bayar a lokacin ba.

Haka zalika a daidai lokacin ne aka yi shari’ar nan ta matashin nan Khalifa D Ado, wanda ake zargin ya tattara miliyoyin kudin matasa da zummar zai samar mu su aiki mai maiko, amma bulunbukwi Khalifa Adon ya cinye kudin kamar yadda aka yi zargi, shima kuma an kama shi an gurfanar dashi a gaban Aminu Gabari, kuma da ya ke ance shari’a sabanin hankali sai gashi shi Khalifa Aminu Gabarin ya bayar da belinsa.

Sai gashi itama wannan baiwar Allah ta gurfana a gaban alkali Aminu Gabari, kuma tun a baya yan uwa sun ce ta gamu da ciwon zuciya ne sakamakon matsalar wannan bashi ,kuma tun  agaban alkalin ta dinga kwarara aman jini.

Amma a haka ya ce a mika ta kurkuku, duk wani roko da mahaifiyar ta dattijuwa Haj uwa tayi tace alkalin ina ai sai ta tafi kurkuku,dan haka mahaifiyar ta hajia uwa ke rokon mai girma cif jojin jihar Kano justice Nura sagir Umar da ya taimaka ya sa baki.

To amma akan wannan batu mun tuntubi Baba Jibo Ibrahim kakakin babbar kotun jihar Kano, wanda ya ce zasu yi bincike akan wnanan batu

DSC Musbahu Lawal Kofar Nasarawa shi ne kakakin hukumar lura da gidajen gyaran tarbiya da a baya ake cewa gidajen yari ya ce su kansu wannan al’Amari ya ba su mamaki domin har yanzu matar sharara amai take a cikin kurkuku

Barrista Badiha Abdullahi lauya ce mai fafutukar kare hakkin dan adam ta ce abin da yafi bashi ma ana bayar da belinsa balle wannan gashi ana gani akwai rashin lafiya

Har ila yau mun zata da wata mata da itama tayi zaman kurkuku kuma kuma dakinsu aka kai Maryam lokacin dake ta yin aman jinin tayi mana Karin haske kn abin da ta gani.

A karshe masana a fannin shari’a na rokon mai girma cif joji da ya duba wannan matsala ya kuma kaddamar da bincike kan irin shari’o’in da ake kaiwa gaban wannan alkali da yadda ake tafiyar da su domin dai samar da sa’ida ga alumma.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!