Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Ana zargin ana tafka cakwakiya a makarantar koyon aikin jinya ta Madobi

Published

on

Wata cakwakiya wacce ta dade tana faruwa a jihar Kano kuma har wannan lokaci an rasa wani babban mutum da zai yi tsawa domin kwato hakkin dalibai.

Wato kamar yadda aka sani dai kwalejin koyon aikin jiyya da Unguwar Zoma dake nan kano da Madobi makaranta ce mai farin jinni, wacce duk shekara dalibai ke rububin samun gurbin karatu a cikinta.

To amma abin takaici da mamaki shi ne,a ka’idar dokar da hukumar lura da wadannan makarantu ta samar, sh ine kowacce makaranta akwai iyakar daliban da aka ba ta dama ta dauka alalal misali a Kano School of Nursing dalibai 100 aka yarda ta diba duk shekara.

Ita kuwa Madobi dalibai 70 kawai aka sahale su diba, to amma la’ akari da yadda kowa ke kaunar shiga makarantar sai ya zama duk shekara sai a buga dubunnan fom a sayar naira dubu 22, daga nan kuma a dauki dalibai sama da dubu 2 a ba su takardar dauka a ba su dama su yi karatu.

Sai bayan wani lokaci ana karatun sai ayi wata jarrabawa da ake cewa weeding a lokacin ne za a kori daliban nan a debi guda dari kacal kaga ragowar sun biya kudin fom da kudin rajistration a bala baiu.

Wannan al’Amari ne ya sa hukumar lura da wadannan makarantu ta rubuto wasika tun ranar 23 ga watan jiya suka hana wannan kwace ,to amma abin takaici a Litinin din nan sai da makarantar ta shirya irin wannan jarrabawa akai domin sallamar dalibai.

Me sauraro idan baka gane ba ,fa ana amfani da wanaan hanya ce wajen samun kudaden shiga batun yadda ake kasafta su kuma wannan Allah ne masani.

Abba Dalha Soron dinki shi ne kakakin makarantar ta koyon aikin jinya kuma shi ne Shugaban malam Gambo Ahmed ya wakilta a matsayin wanda zai Magana da yawunsa ya ce, ai ita waccan hukuma ba ta da hurumin hana kwasar dalibai da yin jarrabawar zubar gade.

Yanzu haka dai wannan karya doka da makarantar ta yi ya na iya jawowa a rufe makarantar tsahon shekaru, sannan kuma wani abu da ya kamata a duba shi ne shin nawa aka tara a bana kuma ina aka kai kudin?

Haka kuma wata majiya ta ce yau an zauna da shugabannin makarantun a ofishin sakataren gwamnati, har ma sauran jagororin makarantar su ke zargin shi shugaban da yin gaban kansa wajen tafiyar da harkokin makarantar.

A waje guda kuma wasu daga cikin ma’aikatan makarantar na kuka bisa yadda su ka ce shi shugaban ya dade da yin ritaya amma abokantakarsa da Excelency ta sa aka sake bashi shugabancin makarantar.

lamarin da su ka ce shima ya saba da doka, kawai sun hakura ne domin fadan da yafi karfin ka sai ka mayar dashi wasa, wani abu da shima ake ta kuka dashi shi ne bisa doka sai mai digiri a fannin aikin jiyya ne kadai aka aminta ya jagoranci irin wannan makaranta .

Yayin da suke cewar a tambaya shin shi Provost na yanzu ya cika wannan kaida? Zamu cigaba da bibiya a gaba watakila ma ku jimu da wnanan amsar.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!