Labarai
Bauchi: Yan sanda sun ta kama wadanda da ake zargi da satar Babura

Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta kama wasu da ake zargi da satar babura a garin Yuli.
Hakan na cikin sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sanda a Jihar Bauchi SP Nafiu Habib ya fitar aka rabawa manema labarai.
A cewar sa lamarin ya faru ne bayan da wasu suka kai hari ga wani mai babur da guduma tare da kwace masa babur, inda jami’an ’yan sanda suka bi sawun su tare da kama Adamu Abubakar da ake kira Abbati mai shekaru 21 tare da kwato babur din.
Sanarwar ta ce, bincike ya kai ga kama Habibu Dauda da ake kira Commander mai shekaru 32 da ake zargi shugaban masu satar ne, tare da kama Abdurrahman Abubakar da Zubairu Garba da ake zargi sun yi yunkurin sayen babur din, inda aka kuma kwato kudi naira dubu dari hudu daga wajen su.
You must be logged in to post a comment Login