Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Bin ƙaƙidar tuƙi zai rage yawaitar haɗɗura akan tituna – Shugaban Injiniyoyi

Published

on

Ƙungiyar Injiniyoyi masu gina gidaje tituna da gadoji ta reshen jihar Kano ta shawarci al’umma da su mayar da hankali wajen bin ƙaƙidojin tuki a fadin jihar Kano dama ƙasa baki ɗaya domin kaucewa daga hatsarurruka akan tituna.

Shugaban ƙungiyar reshen kano Injiniya Murtala Alhaji Garba ne yayi wannan jawabin yayin taron ƙarawa juna sani da suka shirya domin ƙara faɗakar da al’umma kan yadda zasu kare kan su daga haɗɗura a ababan hawa musamman mota akan tituna.

Wannan na zuwa cikin wani ɓangare da ƙungiyar lafiya ta duniya ta ware duk ranar 10 ga mayu a matsayin ranar tunawa da lafiyar hanya domin tabbatar da an samar da hanyoyin masu inganci da gine gine.

A yayin gabatar da makalar an faɗakar da al’umma kan yadda zasu dunga anfani da maɗaurin kujera na mota da sauran abubuwan da ya kamata al’umma su rinƙa kula da zarar sun shiga mota domin kare kai.

Ka zalika an gayyaci injiniyoyi masana aikin hanya gine gine da gadoji domin ƙarin haske kan yadda za’a dunga sanya ido akan ayyuka domin samar da ingantattun ayyukan a faɗin ƙasar nan, inda suka ce yawaita duba ayyukan titi akai akai da samar da kwararru wajen yin tituna zai saukaka wajen rage hatsura akan hanyoyi.

Haka kuma anyi kira ga injiniya da su mayar da hankali sanya idanu yayin da ake gudanar da ayyukan hanya domin samin ingantattun hanyoyi.

Daga ƙarshe an shawarci al’umma da su mayar da hankali wajen bin ƙaƙidojin tuki a wannan lokaci dake yawaitar samin hatsari akan tituna.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!