Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

MARSHAL:Hukumar FRSC ta ce zasu ci gaba da aikin Tallafawa Al’ummah

Published

on

Hukumar kiyaye afkuwar haɗɗura ta ƙasa reshen Kano ta buƙaci al’umma da su kasance masu mayar da hankali wajen tallafawa al’ummar da suka sami haɗɗari musamman a yayin da su ke tafe akan hanya domin samar musu da taimakon gaggawa

Shugaban da ke kula da ɓangaren sa kai na hukumar Alhaji Abdulhadi Umar Ahmad ne ya bayyana hakan a yau yayin taron tunatarwa da hukumar ta shirya domin ƙara wayarwa da al’umma kai kan aikin da sukeyi

Alhaji Abdulhadi Umar Ahmad ya ƙara da cewa suna fatan al’umma zasuyi duba da irin wannan aiki da MASHAl suke yi na taimakon don Allah domin suma su bada irin tasu gudummawar

Da ya ke jawabi mai magana da yahun hukumar Alhaji Salman ya ce wannan aikin da suke aiki ne da shukeyi kyauta domin Allah da kuma bayar da gudummawa ga al’umma musamman akan tituna domin neman taimakon gaggawa

Salman ya ƙara da cewa yana kira ga al’umma da suma suyi huɓɓasa wajen zuwa wannan hukuma domin bayar da ta su gudummawar ga al’umma

Ka zalika ya ce wannan aiki na saka kai ba wai hakan na nufin ƙasƙantar da kai bane kasancewa ba wai sai baka da aiki bane zaka shigo aikin nasu ba ne kasancewar ko mutun ma’aikaci ne zai iya shigowa domin bayar da tasa gudummawar

Daga ƙarshe an karrama wasu daga cikin ƴaƴan hukumar da suka dade suna bayar da gudummawa ga al’umma

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!