Connect with us

Labarai

Biyu daga cikin yan takarar kujerar gwamna a jihar Osun sun janye bukztzr su

Published

on

Biyu daga cikin yan takarar gwamnan jihar Osun sun janye daga takarar gwamnan jihar wanda tun da fari suke bukatar jam’iyyar ta tsayar da su a yayin zaben fidda gwani.

Sakataren gwamnatin jihar Moshood Adeoti da kuma shugaban hukumar kula da ma’aikatan kananan hukumomin jihar Peter Babalola ne suka janye daga bukatar tsayawa takarar bayan da suka bayyana bukatar su tun da fari.

Mutanen biyu sun bayyana janyewar ta su ne, jim kadan kafin fara zaben fidda gwani na gwamnan jihar a yau Juma’a.

Sakataren gwamnatin jihar ya bayyana janyewar tasa ne ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin kungiyar yakin neman zaben sa Mr. Kayode Agbaje wadda aka rarraba wa manema labarai.

Sannan ya ce ya yi hakan ne don samun maslaha da kuma ciyar da jam’iyyar ta su gaba.

Zaben fidda gwani na gwamnan jihar Osun karkashin jam’iyyar APC za’a yi shi ne a mazabu 332 da ke fadin jihar, inda kuma shugabancin jam’iyyar na kasa ya nada wani kwamitin mai kunshe da sanatoci karkashin jagorancin gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari za su isa jihar don sanya idanu kan yadda zaben fidda gwanin zai gud ana.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!