Labarai
Borno: Sojoji sun hallaka kwamandan yan ta’adda da mukarrabansa

Dakarun sojin Najeriya, sun kashe babban kwamandan ‘yan ta’adda Amirul Fiya, wanda aka fi sani da Abu Nazir, tare da wasu yan ta’adda a ƙaramar hukumar Kala-Balge, da ke jihar Borno.
Mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanal Appolonia Anele, ce ta bayyana hakan ta na mai cewa, lamarin ya faru ne bayan dakarun sun fatattaki ‘yan ta’addan ISWAP jim kadan bayan sun shirya kai wani mummunan hari a makon da mukai bankwana da shi.
Haka kuma ta ce, bayan dakarun soji sun fatattaki ‘yan ta’addan, sun gano gawarwakin uku ciki har da shugaban yan ta’addan.
Ta kara da cewa, sun samu nasarar kwato bindiga kirar AK-47, da bama-bamai sai kuma makaman rokoki guda biyu.
Madam Appolonia Anele ta kara da cewa, wannan na daga cikin nasarorin da suke samu a ayyukansu na yaki da ta’addanci a fadin Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login