Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

BRUNO FERNANDEZ : Magajin Messi da Ronaldo

Published

on

An haifi Bruno Miguel Borges Fernandes a birnin   Maia, Porto da ke kasar Portugal a ranar 8 ga watan Satumban 1994.

Ba ya ga wasanni da yayi a mataki na matashi ya kuma fara wasa ne a matsayin cikakken dan wasa a kungiyar Novara a kakar wasa ta shekarar 2012 zuwa 2013. Ya kuma yi wasanni 23 tare da zura kwallaye 4.

Daganan ya zarce kungiyar UDINESE da ke kasar italiya, inda ya kwashe tsawon shekaru 3, tsakanin shekarar 2013 zuwa 2016. Ya kuma yi wasanni 86 sannan ya zura kwallaye 10.

Bruno Fernandez ya sake sauya sheka zuwa kungiyar Sampdoria da ke kasar ta Italiya a matsayin aro daga shekarar 2016 zuwa 2017, ya kuma yi wasanni 33, sannan ya zura kwallaye 5.

Tauraruwar Bruno ta kara haskakawa lokacin da ya sauya sheka zuwa kungiyar Sporting Lisbon da ke kasar-sa ta Portugal, tsakanin shekarar 2017 zuwa watan fabrairun bana (shekarar 2020). Ya kuma yi wasanni 83 tare da zura kwallaye 39.

A wannan shekara Bruno Fernandez ya sauya sheka zuwa kungiyar Manchester United inda yayi wasanni 14 a gasar Firimiyar Ingila sannan ya zura kwallaye 8 tare da taimaka a zura guda 7.

Bugu da kari tun da ya zo kungiyar Manchester united ba ta yi rashin nasara ba a gasar firimiya cikin wasanni 14 da ta yi ta samu nasara a tara ta yi canjaras a 5.

Bruno Fernandez ya kuma lashe kyautar gwarzon dan wasan firimiya har sau biyu a gasar firimiya a watan Fabrairu da Janairu. Wannan ya sanya ya zama cikin fitattun ‘yan wasa a tarihi da suka taba kafa wannan tarihi.

A bangare guda kuma Bruno Fernandez ya lashe kyautar gwarzon wanda ya fi zura kwallo mafi kwarancewa a gasar firimiyar Ingila.

Ya gasar Europa ta nahiyar turai Bruno Fernandez ya zura kwallaye bakwai wanda hakan ta bashi damar kasancewa da ke kan gaba a yawan kwallaye a gasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!