Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari na jagorantar taro kan sha’anin tsaro

Published

on

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na jogarantar taron majalisar ƙoli kan sha’anin tsaro a fadar sa da ke birnin tarayya Abuja.

Daga cikin  wadanda suka  halarci taron sun haɗa da mataimakin shugaban ƙasa  Farfesa Yemi Osinbajo, da  shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

Sai mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya da babban hafsan tsaron ƙasar nan Janar Lucky Irabor.

Sauran sun haɗar da  shugaban hafsan soji  da na ruwa da kuma babban Hafsan sojin sama,  sai  sufeto janar na ƴan sanda Usman Baba Alƙali.

Kafin a fara taron sai da shugaba Buhari ya yi wa Laftanar Kanar Yusuf Mukhtar Dodo ado da sabon mukaminsa na Kanar a ranar Alhamis 25 Nuwambar 2021.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!