Labarai
Buhari ya amince da sabon tsarin albashi ga malaman makarantu a kasar nan
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da biyan malaman makaranta sabon tsarin albashi a kasar nan.
Shugaba Buhari ya bayyana haka a yau litinin yayin taron bikin ranar malamai ta duniya ta bana.
Buhari ya kuma kara musu wa’adin shekarun aiki daga shekara talatin da biyar zuwa shekaru arba’in a matsayin shekarun barin aiki.
Ministan ilimi Malam Adamu Adamu, wanda kuma shi ne ya wakilci shugaba Buhari yayin bikin na bana, ya ce gwamnati ta amince da karin albashin domin karfafawa malaman gwiwa wajen koyar da ilimi mai inganci.
Ana gudanar da ranar tunawa da malamai a duk ranar biyar ga watan Oktoban ko wance shekara, kuma an fara gudanarwar a shekarar 1994, domin tunawa da gudunmawar da malamai ke bayarwa a fannin ilimi.
You must be logged in to post a comment Login