Connect with us

Labarai

Buhari ya fara bai wa matan karkara tallafin Dubu Ashirin-Ashirin

Published

on

Buhari ya fara bai wa matan karkara tallafin Dubu Ashirin-Ashirin

Gwamnatin tarayya ta fara bai wa matan karkara tallafin dubu ashirin-ashirin a jiya asabar.

An fara shirin ne a jihohin Borno da Yobe.

Akalla matan karkara dubu biyar da dari takwas da arba’in ne za su amfana da tallafin a jihar Borno, yayin da dubu uku da dari hudu za su ci gajiyar tallafin a jihar Yobe.

Da ta ke zantawa da manema labarai a gidan gwamnatin jihar Borno jim kadan bayan kaddamar da shirin, ministar kula da harkokin jinkai, dakile abkuwar ibtila’I, Hajiya Sadiya Umar Faruk, ta ce, shirin wani bangare ne na yunkurin da gwmanatin tarayya ke yi wajen rage fatara tsakanin al’ummar kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!