Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan Bindiga sun kashe makiyaya Shida a jihar Osun

Published

on

Akalla Fulani makiyaya shida ne ‘yan bindiga suka kashe su yayin wani hari da suka kai musu a matsugunansu da ke kauyen Wasinmi a yankin karamar hukumar Irewole a jihar Osun.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a daren jiya asabar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, jim kadan da isar ‘yan bindigar kauyen ne sai kawai suka bude wuta kan mai uwa da wabi, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane shida.

Bayanai sun ce hudu daga cikin wadanda ‘yan bindigar suka kashe ‘yan gida daya ne.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike kan faruwar lamarin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!