Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya fitar da jadawalin shirin rage radadi ga ‘yan Najeriya

Published

on

A wani mataki na tallafawa al’umama sakamakon annobar Corona, gwamanatin tarayya ta fitar da jadawalin fara yin rijistar shirin rage radadi a yau litinin.

Cikin wata sanarwa da Ofishin kula da ayyukan na tarayya ya fitar jiya lahadi a Abuja, ya ce, za’a bude shafin yin rijistar da misalin karfe goma na daren yau litinin.

Ofishin kula da ayyukan na tarayya ya fitar da jadawalin wadanda zasu yi rijistar zuwa kaso uku domin rage cunkosu a shafin ya yin yin rijistar a yau litinin.

A cikin jerin wadanda za su amafa da shirin akwai masu neman tallafin kudaden makaranta  da za su fara cikewa da misalin karfe goma na dare yau.

Yayin da ‘yan-kasuwa masu manyan masana’antu kuma zasu fara cikewa a ranar juma’a ashirin da biyar ga watan nan da muke ciki na Satumba da misalin karfe 12 na dare.

Kazalika za’a kara bude shafin a ranar Litinin Ashirin da takwas ga watan nan, ga masu kananan sana’o’in dogaro da kai.

Haka kuma ofishin ya ce ga masu sha’awa da zarar an bude shafin za su iya yin rijista a shafin internet www.survivalfund.ng.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!