Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Buhari ya nada sabon Magatakarda hukumar shirya jarabawar NECO ta kasa

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nada Farfesa Dantani Wushishi a matsayin sabon magatakarda kuma Babban Jami’in Hukumar Kula da Jarabawar NECO ta Kasa.

Hakan na cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Ministan ilimi, Adamu Adamu kuma ya rabawa manema labarai a Abuja.

Sanarwar ta ce, an nada Farfesa Wushishi ne sakamakon mutuwar tsohon magatakardar hukumar Farfesa Godswill Obioma a kwanakin baya.

Yayin da yake taya shi murna, Adamu Adamu ya bukaci sabon Shugaban Hukumar da ya tabbatar da cancantarsa ta hanyar daukaka hukumar shirya jarabawar don yin gogayya da takwarorinta a duniya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!