Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya sha alwashi kawo karshen sace-sacen dalibai a Najeriya

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi shirin daukar mataki na musamman wanda zai kawo karshen sace-sacen dalibai a kasar nan.

Shugaban kasar wanda ya samu wakilcin ministan sifirin Jiragen sama Sanata Hadi Sirika ya bayyana hakan ne a garin Gusau babban birnin jihar Zamfara bayan wata ziyarar jaje da tawagar gwamnatin tarayya ta kai wa al’ummar jihar game da sace daliban.

Ya ce gwamnatin tarayya ta bullo da sabbin dabaru wanda za ayi amfani da su wajen shawo kan matsalar rashin tsaro a kasar nan.

A cewar shugaban kasar ya kadu matuka da jin labarin sace daliban a don hakan ne ya sa ya tashi haikan wajen ganin wannan matsala ba ta sake faruwa ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!