Labarai
Buhari ya tafi ƙasar Amurka don halartar taron Majalisar ɗinkin duniya

Da safiyar Lahadin nan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bar Abuja zuwa Amurka don halartar taron majalisar dinkin ɗuniya karo na 76.
Rahotonni sun tabbatar da cewa a ranar 14 ga Satumba aka fara gudanar da taron.
Taken taron a bana shi ne “Inganta rayuwa don farfaɗo wa daga cutar corona”.
Ana sa ran shugaba Buhari zai yiwa Majalisar jawabi a ranar Juma’a 24 ga Satumba kan al’amuran da suka shafi duniya baki ɗaya.
M kiai magana da yawun shugaban Femi adesina ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa a ranar Asabar.
Ya ce shugaba Buhari da mukarrabansa za su kasance cikin wasu muhimman taruka.
A cewar hadimin shugaban kasar, ana sa ran shugaba Buhari zai dawo Najeriya a ranar Lahadi 26 ga Satumba.
You must be logged in to post a comment Login