Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sauyin yanayi: Buhari zai tafi ƙasar Scotland

Published

on

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai tafi birnin Glasgow na ƙasar Scotland.

Buhari zai halarci taro karo 26 wanda majalisar ɗinkin duniya ta shirya kan batun sauyin yanayi.

Mataimakin shugaban kan harkokin yaɗa labarai Malam Garba Shehu ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Shehu cikin sanarwar ya ce, shugaban ƙasa Buhari zai gabatar da jawabinsa a taron a ranar 2 ga watan Nuwamba.

Ana sa ran jawabin na sa zai bayyana muhimman abubuwan da Najeriya ta sa a gaba, da kuma matakin da za ta ɗauka na tunkarar sauyin yanayi da ma irin ci gaban da ƙasar ta samu kan matsalolin sauyin yanayin da ake fuskanta.

Shehu ya bayyana cewa taron da kasar Birtaniya ta shirya tare da hadin gwiwar Italiya, zai haɗa bangarorin da za su taimaka wajen gaggauta daukar matakai kan yarjejeniyar Faris da kuma yarjejeniyar majalisar ɗinkin duniya kan sauyin yanayi.

Haka zalika sanarwar ta ce, shugaba Buhari zai halarci wasu taruka da shugaban Amurka Joe Biden da na Faransa Emmanuel Macron za su shirya.

Garba Shehu ya kuma ce shugaban zai samu rakiyar ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama, da ƙaramar ministar muhalli Sharon Ikeazor, dai mai bada shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno da Darakta Janar na hukumar leƙen asiri Ambasada Ahmed Rufai Abubakar.

Bayan kammala taron, Buhari zai tafi birnin Faris na ƙasar Faransa don halartar taro kan batun zaman lafiya, sai dai sanarwar ba ta bayyana ranar dawowar sa ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!