Labarai
Buhari ya umarci jami’an Civil Defence su koma gadin makarantu
Gwamantin tarayya ta umarci hukumar tsaro ta Civil Defence, da ta fito da sabbin tsare tsare da zai taimaka wajen bada tsaro ga makarantun kasar nan.
Wannan dai na zuwa ne a lokaci guda da ake ci gaba da samun yawaitar hare-haren ‘yan bindiga wadanda ke sace dalibai a arewacin kasar nan.
Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya ba da wannan umarnin a jiya a birnin tarayya Abuja, lokacin da ya ke ganawa da sabon shugaban hukumar tsaron ta Civil Defence, Ahmed Audi.
Aregbesola, ya ce, abin takaici ne yadda ake samun yawaitar satar dalibai a baya-bayan nan
‘‘Sabon salon da ‘yan bindigar suka fito dashi wajibi ne mu dakile shi, adon haka lokaci yayi da hukumar tsaro ta Civil Defence za ta hada kai da sauran hukumomin tsaro don samar da tsaro a makarantun kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login