Connect with us

Labarai

Buhari ya umarci jami’an Civil Defence su koma gadin makarantu

Published

on

Gwamantin tarayya ta umarci hukumar tsaro ta Civil Defence, da ta fito da sabbin tsare tsare  da zai taimaka wajen bada tsaro ga makarantun kasar nan.

Wannan dai na zuwa ne a lokaci guda da ake ci gaba da samun yawaitar hare-haren ‘yan bindiga wadanda ke sace dalibai a arewacin kasar nan.

Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya ba da wannan umarnin a jiya a birnin tarayya Abuja, lokacin da ya ke ganawa da sabon shugaban hukumar tsaron ta Civil Defence, Ahmed Audi.

Aregbesola, ya ce, abin takaici ne yadda ake samun yawaitar satar dalibai a baya-bayan nan

‘‘Sabon salon da ‘yan bindigar suka fito dashi wajibi ne mu dakile shi, adon haka lokaci yayi da hukumar tsaro ta Civil Defence  za ta hada kai da sauran hukumomin tsaro don samar da tsaro a makarantun kasar nan.

 

 

 

 

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!