Connect with us

Labarai

Buhari yayi ganawar sirri da Jonathan

Published

on

A dazu dazunnan ne dai Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala wata ganawar sirri da tsohon tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yau a fadarsa ta Villa da ke Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa da karfe uku na wannan rana ne Goodluck Jonathan ya iso fadar ta shugaban kasa kuma kai tsaye ya zarce zuwa ofishin shugaban kasa muhammadu Buhari.

Sai dai har ya zuwa wannan lokaci babu wani cikakken bayanin makasudin ziyarar ta tsohon shugaban kasa Jonathan ga shugaba Buhari.

Sai dai bayan fitowar daga ganawar, tsohon shugaban kasa Jonathan ba ice komai ba, amma dai ya gaisa da sauran ma’aikatan fadar ta shugaban kasa.

Wannan dai shi ne karo na biyar da Goodluck Jonathan ke ziyartar fadar ta shugaban kasa, sai dai ziyararsa ta karshe kafin yau ita ce tun a shekarar 2016.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 332,894 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!