Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari zai gina asibiti mai gadaje 14 a fadarsa

Published

on

Gwamnatin tarayya za ta gina asibiti a fadar shugaban kasa da zai dauki gadaje 14.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da gina asibitin kamar yadda babban sakataren fadar shugaban kasa, Alhaji Umar Tijjani ya bayyana yayin da yake kare kasafin kudi a gaban kwamitin majalisar dattawa.

Ya ce ginin asibitin na fadar shugaban kasar zai lakume kudi kimanin naira biliyon 21.9.

A ranar litinin 1 ga watan Nuwambar 2021 ne za a fara aikin gina asibitin wanda aka baiwa kamfanin Julius Berger aikin.

Ya kuma ce za a kammala aikin ne a watan Disambar shekara mai kamawa ta 2022.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!