Labarai
Buhari zai tafi ƙasar Belgium
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja, a yau Talata domin halartar taron shugabannin ƙasashen Turai da na Afirka da kuma shugabannin ƙasashe da dama a taron kungiyar Tarayyar Turai da Afrika karo na shida a birnin Brussels na ƙasar Belgium.
Taron wanda zai gudana tsakanin 17 da 18 ga watan Fabrairun 2022, zai mayar da hankali wajen tattaunawa kan batutuwan da suka shafi duniya a halin yanzu.
Cikin batutuwan kuwa sun haɗar samar da kuɗin ciyar da ƙasashen gaba, batun sauyin yanayi da samar da makamashi da harkokin sadarwa da tattalin arziƙi.
Sai kuma batun sufuri harkokin tsaro sha’anin mulki da kuma haɗin kan kasashe da sauran batutuwa.
Shugaban Buhari zai yi amfani da damar taron wajen ƙalla alaka da wasu kasashen duniya biyu, kuma zai samu rakiyar ministan harkokin Waje Geoffrey Onyeama da na Lafiya Dr Osagie Ehanire da ƙaramar ministan Muhalli, Sharon Ikeazor.
Sai mai bashi shawara kan harkokin tsaro, Manjo janar Babagana Monguno mai ritaya, da Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa Ambasada Ahmed Rufa’i Abubakar da shugabar hukumar kula da ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje Abike Dabiri-Erewa.
Ana sa ran shugaba Buhari zai dawo Najeriya a ranar Asabar.
You must be logged in to post a comment Login