Connect with us

Labarai

Bukola Saraki:ya bada tabbacin marawa hukumar EFCC baya

Published

on

Shugaban majalisar dattijai Abubakar Bukola Saraki, ya bada tabbacin marawa hukumar EFCC baya, da nufin inganta hukumar ta hanyoyin daban-daban, don yakar cin hanci da rashawa.

Wannan na kunshe cikin sanarwar da Sakatarensa na musammam kan kafafen yada labarai Sanni Onogu ya fitar.

Sanarwar ta kara da cewa, Shugaban ya furta hakan ne lokacin ya da ka kai ziyarar gani da ido zuwa sabon shelkwatar hukumar EFCC da ake ginawa a birnin tarayya Abuja.

A Sanarwar, Bukola Saraki ya yi matukar gamsuwa da tsarin sabon ginin, duba da cewa an yi tsari ginin ne, da taimakon kwararu kan harkan gine-gine na kasar nan.

Ta kuma ce, ziyara ta sa, wani bangare ne da ke nuna damuwar majalisun tarayyar kasar nan na ci yar da kasar nan gaba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!