Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Bundesliga: Kano ce cibiyar gasar a Arewacin Najeriya – Henning Brinkmann

Published

on

Masu shirya gasar bundesliga ta kasar Jamus sun fitar da wani sabon tsari ga magoya bayan gasar a Nigeria.

Wakilin gasar Henning Brinkmann ya bayyana hakan ga manema labarai, yana mai cewa Bundesliga ta hada kai da gidajen Rediyo a jihar Kano musamman Freedom Rediyo don kawo wa magoya baya yadda wasannin ke kasancewa kai tsaye.

Brinkmann ya ce Nigeria na daya daga cikin kasashen da Bundesliga ta mayar da hankali wajen fadada ayyukan ta don haka zasu cigaba da shirya taruka don farantawa magoya bayansu.

“Manufar ita ce sanya masoya su kara jin dadin gasar duba da jihar Kano ce cibiyar kwallon kafa a Nigeria kamar yadda bincikenmu ya nuna, hakan ne ya sanya za mu kawo wasu sabbin abubuwa a jihar dama sauran wasu jihohi a kasar,” inji Brinkmann.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!