Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Burina taka leda a Barcelona – Ibrahim Sa’id

Published

on

Tsohon dan wasan kungiyar Kwallon kafa ta matasa ‘yan kasa da shekaru 17 ta Kasa , Golden Eaglet Ibrahim Said , ya ce ya shirya tsaf don bugawa kowacce kungiya da ta mallake shi a matsayin dan wasa a nahiyar Turai da zarar an dawo harkokin Kwallo ta kuma kankama.

Ibrahim Said, ya bayyana haka ne a yayin zantawar sa da manema labarai a yau, Jim kadan bayan bikin murnar cikar dan wasan shekaru 18, daya gudana don taya shi murna.

Ibrahim Saida, wanda dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Dabo Babes, ne ya samu tsaikon sauya sheka zuwa taka Leda a Turai sakamakon tsaida harkokin wasanni da Annobar Cutar Corona ta haddasa a fadin duniya .

Ibrahim Said, na daya daga cikin ‘yan wasan kasar nan da tauraruwar sa ta haska , a gasar cin kofin duniya na matasa da aka kammala a kasar Brazil , a shekarar data gabata inda ya zura kwallaye uku a wasan cikin rukuni da Najeriya ta fafata Ecuador.

Ibrahim Said, ya ce ya shirya yanzu haka da zarar komai ya dai-dai ta, kuma zai iya buga kowacce lamba matukar an bukaci hakan ,in ka dauke tsaron raga, sai dai yace ya fi son bugawa a gefen dama daga gaba.

Burina na samu kungiya a Turai, amma in son samu ne na wakilci Barcelona, don ita ce kungiyar da nake so tare da bibiya saboda Lionel Messi, inji Ibrahim Said.

Ya kara dacewa ya na son su ne, saboda salon wasan su na murza kwallo daya bayan daya, kuma ina fatan buga musu wasa a nan gaba ba da dadewa ba.

Nagodewa ‘iyayena ‘yan uwa da abokanan arziki, da masu horar dani da sauran abokanan kwallo da muke fadi tashi, muna fatan wannan annoba zamu ga karshen ta bada dadewa ba, don cigaba da abinda muka saka a gaba, inji matashin dan wasan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!