Connect with us

Labarai

CBN: zai janye kudaden da suka lalace daga hannu jama’a

Published

on

Babban bankin kasa CBN ya ce zai janye kudade da su ka lalace daga hannun jama’a, wadanda yawansu ya kai kusan naira tiriliyan takwas.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakin gwamnan babban bankin kasa CBN Folashodun Shonubi da kuma daraktar kudi na babban bankin Mrs Priscilla Eleje.

Sanawar ta ce kudaden sun yi lalacewar da na’urorin ciran kudi na banki wato ATMs basa iya gudanar da hada-hada da su.

A cewar sanarwar, a gobe talata, gwamnan babban bankin kasa CBN Godwin Emefiele zai kai ziyara Lagos don kaddamar da sabon tsarin sabbin takardun kudi.

Bankin na CBN ya ce wannan wata hanya ce ta dakile lalacewar takardun naira.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,812 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!