Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu ci gaba da sauya wa mutanen karkara sabon kudi har zuwa 31 ga wata- CBN

Published

on

Babban bankin ƙasa CBN, ya ce, zai ci gaba da sauya wa mazauna yankunan karkara kuɗi a hannu domin sauƙaƙa musu samun sababbin kuɗin.

Mataimakin Daraktan babban bankin da ke Abuja Engr Muhammad Alii, ne ya bayyana hakan a ganawar sa da wakilinmu Auwal Hassan Fagge a garin Bunkure yayin ci gaba da aikin sauya wa mutane kuɗi a hannu.
Haka kuma ya ƙara da cewa za su ci gaba da zagaya wa domin sauya kuɗaɗen har zuwa kasuwanni.

A nasu ɓangaren, wasu daga cikin mutanen da aika sauya wa kuɗin sun bayyana jin dadinsu bisa samun sababbin takardun kudin na Naira dubu goma ga kowane mutum, suna masu cewa hakan zai sauƙaƙa musu wahal

A nasa ɓangaren, Sarkin Shanun Rano Hakimin Kibiya, Alhaji Abubakar Sunusi Abubakar Ila, yayin da tawagar ta CBN da jami’an bankunan kasuwanci suka kai ziyara fadarsa, ya bayyana farin ciki bisa tsarin yana mai cewa zai taimaka wa al’umma matuƙa.

Shugaban tawagar Engr Muhammad Alii, ya kuma shaida wa hakimin cewa, yanzu haka babban bankin ƙasa ya fito da tsarin karɓar kudi domin sauya wa mutanen da ke da su da yawa inda za su riƙa kai wa shalkwatar babban bankin domin a sauya musu da sababbi.

 

Rahoton: Auwal Hassan Fagge

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!