Labaran Kano
Cibiyar nazarin harkokin tsaro za ta koyar da matasa sabbin dabarun tsaro
Cibiyar nazari kan harkokin tsaro mai zaman kanta da ke cibiyar horas da matasa ta Sani Abacha a nan Kano, ta ce za ta bullo da sabbin dabaru wajen dake matsalolin tsaro da ke addabar arewacin kasar nan.
A cewar cibiyar fahimtar halin da ake ciki na rashin tsaro a arewacin kasar nan yasa aka kirkiro da cibiyar wajen horar da al’umma yadda zasu samar da tsaro.
Shugaban cibiyar Dr. Usman Muhammad Jahun ne ya bayyana hakan, jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na tashar freedom rediyo a safiyar yau.
Ya ce, cibiyar na horar da matasa fannonin ilimi da dama, amma sun fi mayar da hankali kan horar da yadda za a dakile matsalar tsaro.
A nasa bangaren Daraktan tsare-tsare na cibiyar, Ahmad Abdul’aziz Chiroma Sumaila, cewa ya yi cibiyar, ta samar da kyakkyawan yanayin karatu, sai dai ya bukaci gwamnatoci a dukkan matakai da sarakunan gargajiya da su sanya hannu don tafiyar da lamarin yadda ya kamata.
Bakin sun kuma yi kira ga al’umma da su shigo cikin tsarin domin samun horo kan yadda zasu kula da unguwannin su.