ilimi
Cin hanci da rashawa ne ya ruguza fannin ilimi a Najeriya – Dakta Bilyaminu
Wani malami a tsangayar ilimi a jami’ar Bayero ta Kano ya ce cin hanci da rashawa na taka muhimmiyar rawa wajen tabarbarewar ilimi a Najeriya.
Dakta Bilyaminu ne ya bayyana hakan ga tashar Freedom Radio.
Ya ce cin hanci a yanzu na gaba gaba wajan durkusar da ilimi idan aka yi duba da matsalolin da a kullum ake gani a fannin ilimi.
Dakta Bilyaminu ya ce “iyaye kan goyi bayan yaransu wajen bada cin hanci ga malamai dan su samu nasara a jarabawa”.
Yana mai cewa iyaye kan biya makudan kudade don a rubutawa yaransu satar amsa musamman lokacin jarabawa kammala Sakandare ta WEAC da NECO”.
Ya kuma ce kamata yayi gwamnati ta rinka fitar da kasafin kudi mai yawa a bangaren ilimi domin inganta shi.
You must be logged in to post a comment Login