Labarai
CISLAC ta soki afuwar da Shugaba Tinubu ta yiwa masu laifin cin hanci, fataucin miyagun kwayoyi da manyan laifuka

Cibiyar Civil Society Legislative Advocacy Centre (CISLAC) ta nuna tsananin adawa da matakin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauka na bayar da afuwar shugaban kasa ga mutane 175, ciki har da wadanda aka same su da laifin fataucin miyagun kwayoyi, hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, manyan laifuka da kuma cin hanci da rashawa.
A cikin wata sanarwa da Daraktan CISLAC kuma shugaban Transparency International Nigeria, Auwal Ibrahim Musa (Rafsanjani) ya sanyawa hannu, kungiyar ta bayyana wannan mataki a matsayin abin da bai dace da doka ba, mara da’a kuma mai bata sunan Najeriya a idon duniya.
An ce cikin jerin wadanda aka yi wa afuwa har da tsohon gwamnan Jihar Delta, James Ibori, wanda aka daure a Birtaniya, da kuma wasu da ake zargi da satar mai, garkuwa da mutane, da fataucin danyen ma’adinai, da sauran laifukan kasa da kasa. CISLAC ta ce bai dace irin wadannan mutane su ci gajiyar afuwa ba, musamman wadanda ba ma a Najeriya aka yanke musu hukunci ba.
You must be logged in to post a comment Login