Labarai
CNG ta yi Alla-wadai da shirin Shugaba Tinubu na sabbin dokokin haraji

Gamayyar kungiyoyin Arewa watau Coalition of Northern Groups CNG, ta yi Allah-wadai da shirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na fara aiwatar da sabbin dokokin haraji daga farkon watan Janairun sabuwar shekarar nan ta 2026, ta na mai bayyana hakan a matsayin hari kai tsaye ga tsarin dimokiradiyya.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a Abuja, inda ta ce akwai banbanci a tsakanin dokokin da Majalisar Dokoki ta amince da su da kuma waɗanda aka wallafa a mujallar gwamnati tana zargin cewa an yi gyare-gyare a cikin dokokin bayan Majalisa ta riga ta amince da su.
Kungiyar ta ƙara da cewa tilasta wa jama’a bin irin waɗannan dokoki da aka ce an canza su bayan an amince da su ya saɓa wa doka da tsarin mulki, kuma hakan na iya haifar da rashin amincewa da tsarin dimokiradiyya a zukatan al’umma.
You must be logged in to post a comment Login