Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

CNG ta yi watsi da roƙon ƴan majalisar Wakilai na neman a saki Nnamdi Kanu

Published

on

Gamayyar ƙungiyoyin Arewa watau CNG, ta yi watsi da kiran da tsagin marasa rinjaye na majalisar wakilai suka yi na neman sakin shugaban haramtacciyar ƙungiyar masu neman ballewa da fafutukar kafa ƙasar Biafara ta IPOB Nnamdi Kanu.

Ƙungiyar ta bayyana buƙatar a matsayin cin zarafi ga waɗanda ake zargin ayyukan Kanu ya shafa da sauran al’ummar Najeriya, inda gwamnatin Najeriya ta kama tare da tuhumar Kanu kan ayyukansa.

A cikin wata sanarwa da CNG ta fitar mai ɗauke da sa hannun babban Jami’inta na ƙasa Kwamared Jamilu Aliyu Charanchi, ya tunasar da irin abubuwan da Kanu ya aikata a baya, inda ta ce ta kai kararsa ga Majalisar Dinkin Duniya ranar 7 ga watan Agustan shekeran 2017, kan ayyukan kungiyarsa, da suka yi zargin na ta’addanci ne.

Sanarwar kuma ruwaito ce, ko da gwamnatin Nijeriya a hukumance ta ayyana IPOB a matsayin ƙungiyar ta’addanci a ranar 27 ga watan Yunin 2021, biyo bayan kama Kanu da kuma tuhume-tuhume da suka shafi tada tarzoma, ɓarnata dukiya, da kuma mutuwar ‘yan Najeriya da dama da jami’an tsaro.

Chiranci ya bayyana matukar kaɗuwarsa bisa yadda ƴan majalisar wakilai, ke goyon bayan a saki Kanu, wanda ake tsare da shi bisa umarninwata kotun da ke da hurumi ba.

Babban jami’in na CNG na ƙasa, ya yi Kira ga ƴan Najeriya da su tashi tsaye wajen yin watsi da irin wannan matakin, kuma ka da su lamunci duk wani abu da zai ta’azza ko kawo wanzuwar ta’addanci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!