Labarai
Colombia ta yi Allah wadai da matakin Amurka na kwace tankar mai ta kasar Venezuela

Shugaban kasar Colombia, Gustavo Petro, ya yi Allah wadai da matakin Amurka na kwace wata tankar mai ta Venezuela, yana mai bayyana hakan a matsayin fashin teku na man fetur.
Petro ya yi gargadin cewar irin wannan katsalandan a yankin Caribbean na iya haifar da tashin hankali da ƙarin rikice-rikice tsakanin ƙasashen yankin.
Gargadin na sa da na zuwa ne kwanaki kadan bayan da jagoran Adawa a Birtaniya Jeramy Corbyn, ya yi irin wannan suka da matakin gwamnatin shugaba Trump ke yi a yankin, musamman ma a kasar ta Venezuela.
Shugaban na Colombia Mr Petro ya yi kira da a mutunta ‘yancin kowace kasa tare da tabbatar da neman mafita ta hanyar diflomasiyya, ba wai nuna karfi ba
You must be logged in to post a comment Login