Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Corona – An dakatar da fara rigakafin Corona zagaye na biyu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta dakatar da fara yin rigakafin cutar corona zagaye na biyu da ta shirya farawa a Talatar nan.

Kwamitin shugaban ƙasa mai yaƙi da cutar ne ya sanar da hakan, ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kwamitin Mr Willie Bassey ya fitar a Abuja.

Kwamitin ya ce, an shirya fara yin rigakafin corona samfurin Moderna waddda ƙasar Amurka ta bai wa Najeriya, a ranar goma ga watan Agustan da muke ciki, don yaƙi da cutar.

Mr Willie Bassey ya ce, ɗage fara rigakafin ya faru ne sakamkon wasu matsaloli da aka samu, wanda a yanzu za afara rigakafin a ranar 16 ga watan Agusta.

Wannan dai na zuwa ne adaidai lokacin da yawan waɗanda suka kamu da cutar corona a Najeriya ya kai dubu ɗari da saba’in da bakwai, da ɗari shida da goma sha biyar.

Wadanda suka rasu sanadiyyar cutar sun kai dubu biyu da ɗari daya da tamanin da biyar.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!